1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin kasashe kan ficewar wasu daga ECOWAS

Nasir Salisu Zango
January 29, 2024

Fashin baki kan matakin Nijar da Mali da Burkina Faso na ficewa daga ECOWAS da kuma yadda zai iya jefa al'ummar yankunan cikin garari da karuwar tabarbarewar tsaro a yankin

https://p.dw.com/p/4bo7I
Wakilan kasashe a wani taron kungiyar ECOWAS a Abuja
Wakilan kasashe a wani taron kungiyar ECOWAS a AbujaHoto: Kola Sulaimon/AFP

Dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen da kuma kungiyar ta ECOWAS tun bayan da sojoji suka hambarar da shugabannin su suka kuma girka mulkin soji. Duk da cewar an dauki lokaci ana zaman cin kunamar kadangare amma abin da yazo da ba zata, sai kawai aka jiyo kasashen sun hade kansu tare da ayyana janyewa daga wannan hadaka ta ECOWAS, matakin da ke ci gaba da jawo martani.

Karin Bayani: Kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun yi bankwana da ECOWAS

Assimi Goita na Mali, Abdourahamane Tiani na Nijar da Ibrahim Traoré na Burkina Faso
Assimi Goita na Mali, Abdourahamane Tiani na Nijar da Ibrahim Traoré na Burkina FasoHoto: Francis Kokoroko/REUTERS; ORTN - Télé Sahel/AFP/Getty; Mikhail Metzel/TASS/picture alliance

Alhaji Amadu Madawa shi ne shugaban 'yan Nijar mazauna Kano, ya bayyana cewar kamata ya yi kasashen su sauya tunani da lissafi domin matakin zai takura al'ummar su da ke mu'ammala kai tsaye da kasashen ECOWAS

To amma a ra'ayin Awwal Musa Rafsanjani shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam Amnesty International a Nigeria, ya ce kungiyar ECOWAS ce ta jawo wannan bore duba da irin gashin kuma da ta ke yi wa kasashen musamman ma jamhuriyar Nijar

Firaministan Mali Choguel Maiga, Nijar Ali Lamine Zein, Burkina Faso Apollinaire Kyelem
Firaministan Mali Choguel Maiga, Nijar Ali Lamine Zein, Burkina Faso Apollinaire KyelemHoto: Balima Boureima/Anadolu/picture alliance

Sai dai kuma a ra'ayin masana a fannin tsaro irin su Dr Yahuza Getso, ya na ganin cewar matakin tamkar bude kofar ta'azzarar matsalolin tsaro ne wadanda suka dade da samun gindin zama a tsakanin kasashen wannan yanki na Afrika ta yamma

Karin Bayani: Tattaunawa ta ci tura tsakanin Nijar da ECOWAS

Ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa a tsakanin kasashen kuwa Dr Abdussalam Kani masanin tattalin arziki a kwalejin ilimi ta Sa'adatu Rimi da ke Kano ya na ganin cewar wannan mataki tonon silili ne ga kasashen da kuma kungiyar ECOWAS kuma zai kara tankada al'ummar yankin cikin matsin tattalin arziki kari akan wanda suke ciki

Masana da sauran jama'a dai na cigaba da fashin baki kan batun wanda tuni masu zirga zirga tsakanin kasashen suka fara tunanin hanyoyin samun mafita.