1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben 2023: Makomar adawa a Najeriya

July 1, 2021

A wani abun da ke zaman alamu na makoma maras tabbas ga jam'iyyun adawa a Najeriya, jam'iyyar APC mai mulki, na ci gaba da karbar gwamnoni da 'yan majilisun tarayya da na jihohi da ke ta sauya sheka daga PDP ta adawa.

https://p.dw.com/p/3vpxS
Nigeria Oppositionspartei APC
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, na samun karuwa daga jam'iyyar adawa ta PDPHoto: DW/K. Gänsler

Akalla gwamnoni uku ne dai ko bayan 'yan majalisun dattawa da wakilai a tarayya da jihohi, suka fice daga jami'iyyar PDP ta adawa ya zuwa APC 'yar mulki a Najeriyar daga bangare dabam-dabam cikin kasar. Duk da cewar dai kusan ya zama al'ada, sauyin shekar a tsakanin jam'iyyun kasar a lokutan da ake fuskantar zabe, komawar kimanin gwamnoni biyu cikin tsawon kasa da watanni biyu dai, na daukar hankali a kasar da ke kallon barazana mai girma.

Karin Bayani: Jam'iyyar APC ta ce ba ta damu da fitar Saraki ba

Akwai dai tsoron babakeren jam'iyya guda daya, na iya sauya makomar dimukuradiyya a Najeriyar da kila kama hanyar yin kama karyar ga 'yan kasar. Alhaji Tanko Yakasai dai ya share lokaci yana taka rawa cikin siyasar Najeriyar da kuma ya ce kokarin kashe gasa a siyasar na barazana har ga makoma ta kasar a nan gaba. Ridda cikin siyasar Najeriya ko kuma  shan koko mai kama da daukan rai dai, sauyin shekar kuma a tunanin Injiniya Buba Galadima da ya share lokaci yana sana'ar ta adawa, na zaman alamun kasawa a bangaren  PDP  da a cewarsa har yanzu ke karatun tatata a adawar.

Nigeria Regierungspartei PDP
Ko babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta shiryawa zaben shekara ta 2023?Hoto: DW/K. Gänsler

Halin da ke kama da zannen dutse, ko kuma gwagwarmaya ta neman mafita a shekarun da ke tafe dai, ana kallon rage karfin na adawa na iya shafar kokarin 'yan lemar na karbe mulki daga APC ta masu tsintsiya. To sai dai kuma a tunanin Sanata Umar Tsauri da ke zaman sakataren PDP na kasa, masu sauyin shekar na zaman azzaluman da ba su iya jure zama a tsarin na adawa.

Karin Bayani: Rikici na kara mamaye siyasar Najeriya

Koma ya take shirin kayawar a makomar ta adawa dai, ga Faruk BB Faruk da ke zaman kwararre a siyasar Tarayyar Najeriyar, rashin akida tsararra ne ya sanya sauyin shekar ke kama da sauyin riga a siyasar kasar a halin yanzu. Ana dai kallon yiwuwar sake tashin sabuwar jam'iyyar ta adawa, ga da dama a cikin 'ya'yan jam'iyyun biyu da ke kusantar zaben shekara ta 2023, ba tare da matabbata ta makoma mai kyau ba.