1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta samu lambar yabo ta Nansen

Abdourazak Maila Ibrahim MAB
October 4, 2022

Tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta samu lambar yabo ta Nansen daga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya saboda yunkurinta na marabtar masu neman mafaka a lokacin da take kan mulki.

https://p.dw.com/p/4Himw
Altkanzlerin Merkel zu Gespräch im Berliner Ensemble
Tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: picture alliance/dpa

A lokacin da yake tsokaci a birnin Geneva, shugaban hukumar ta UNHCR Filippo Grandi ya yaba da kudurin tsohuwar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na kare masu neman mafaka da kare hakkin dan adam tare da yaba mata kan shugabanci na garo da jajircewa da tausayin bil Adama.

Ita dai Merkel za ta karbi kyautar dala 150,000 (Euro 151,500) a yayin wani bikin mika mata kyautar Nansen da zai gudana a Geneva na Switzerland a ranar 10 ga Oktoba. Idan za a iya tunada dai, Jamus ta karbi 'yan gudun hijira sama da miliyan 1.2 da masu neman mafaka, a daidai lokacin da ake fama da rikicin Siriya.