1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Ministar harkokin wajen Jamus tana Gabas ta Tsakiya

Suleiman Babayo ATB
January 8, 2024

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta gana da manyan jami'an gwamnatin Isra'ila yayin da manyan kasashen ke neman hanyar kawo karshen rikicin tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas.

https://p.dw.com/p/4axgZ
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena BaerbockHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock ta gana takwaranta Israel Katz na Isra'ila a birnin Kudus, wanda ya yi gadiya da taimakon da Jamus take bai wa kasarsa, a ci gaba da ziyarar da ministar take yi a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya. Wannan ke zama ziyarar Baerbock ta hudu zuwa Isra'ila tun lokacin da 'yan ta'adda na Hamas suka kai hari kan Isra'ila abin da ya janyo martani mai zafi daga hukumomin Isra'ila.

Haka Antony Blinken Sakataren harkokin wajen Amirka yana ziyara a wannan Litinin zuwa Isra'ila a ci gaba da ziyarar babban jami'in diflomasiyyan na Amirka zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, inda ya je wasu kasashen yankin tare nuna damuwa game da yanayin da Falasdinawa suka shiga sakamakon yakin da ke faruwa.