1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Almajiran Shiekh Al-Zakzaky na murnar dawowarsa

Uwais Abubakar Idris LMJ
February 22, 2024

Shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi na Najeriya Sheikh Ibraheem Yaqoub Al-Zakzaky ya koma gida, bayan jinya da ya yi a kasar Iran.

https://p.dw.com/p/4clWf
Najeriya | Ibraheem Yaqoub Al-Zakzaky | 'Yan Uwa Musulmi | Shi'a | Gwgwarmaya | Iran
An dai yi ta dambarawa da almajiransa kafin a sake shi tare da mai dakin nasaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Dubban 'yan Shi'a 'ya'yan kungiyar ta 'Yan Uwa Musulmi ne suka cika filin wasa na kasa da ke Abuja makil, inda suka yiwa shugaban nasu na a Najeriyar Sheikh Ibraheem Yaqoub Al-Zakzaky tarba ta musamman a lokacin da ya dawo Najeriyar. Watani hudu ya kwashe a kasar ta Iran yana jinya, kafin dawowa Najerya. Tun bayan arangamar da suka yi da sojoji a 2015 a Zaria ne dai, shi da mai dakinsa Zeenatuddeen Ibraheem suke  dauke da harsasai na harbin da aka yi masu. Almajiran nasda manyan da kanana sun kasance cikin farin ciki da nashuwa da dawowar jagoran nasu a Abuja, musamman yadda suka samu izini na amfani da filin wasa na kasa abinda ba kasafai suke samu ba a lokutan baya. Sheikh Ibraheem Al-Zakzaky ya bayyana cewa zai ci gaba da aikin da yake yi, domin babu batun ja baya a  aikin da yake yi tare da almajiransa. Wannan ne dai karon farko da shugaban na kungiyar 'Yan Uwa Musulmi Sheikh Al-Zakzaky ya yiwa dubban almajiransa jawabi, tun bayan arangamar da suka yi da sojoji a Zaria da ta yi sanadiyyar kashe magoya bayansa da dama ciki har da 'ya'yansa uku.