1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Rage radadin talauci ga 'yan Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 6, 2023

A kokarin rage radadin talauci ga al'ummar Najeriya da ke cikin halin matsin tattalin arziki, sabuwar gwamnatin kasar ta dakatar da aiwatar da wasu jerin karin haraji.

https://p.dw.com/p/4TWcJ
Najeriya | Talauci | Yara | Yunwa
Tsananin talauci da fargabar matsalar yunwa a NajeriyaHoto: Adam Abu-bashal/AA/picture alliance

Tun bayan da gwamnati zare tallafin man fetur ne dai, miliyoyin al'ummar Tarayyar Najeriyar ke ta korafin barazanar fadawa cikin kogin babu. Karin farashin man gami da hauhawar kayan da ya haifar dai, na janyo kururwar korafi cikin kasar da ke ta kallon ragin kudin shiga da walwalar al'umma. To sai dai kuma sabuwar gwamnatin kasar ta sanar wasu matakai da ta dauka,ta hanyar rage wasu jerin harajin talakawa da nufin rage radadin babun da ke ta kara yaduwa tsakanin al'umma.

Wannan matakin dai na zuwa ne, a daidai lokacin da kungiyar Likitoci na Gari na Kowa ta ce ana fuskantar barazanar yunwa da karuwar cututtuka a tsakanin yara sakamakon karancin abincin da ke ta karuwa musamman a yankin Arewa maso Yammacin kasar a halin yanzu. Kungiyar dai ta ce daga farkon watan Janairu na shekarar bana ya zuwa watan Mayu an samu karuwar yaran da ke ziyartar cibiyoyin magani da kungiyar da samar a yankin Arewa maso Yamman saboda matsalar yunwa ko kuma ace tamowa. Kungiyar dai ta ce akalla yara dubu 10 da 200 ne da tamowar tai nasarar kwantarwa cikin jihohin Kano da Katsina da Kebbi da Sakkwato baya ga jihar Zamfara.