1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Najeriya: An kafa dokar hana fita a jihar Filato

August 15, 2021

Wani sabon rikici ya barke bayan kisan matafiya Musulmai a jihar Filato ta Najeriya, inda hukumomi suka ga dacewar kafa dokar hana zirga-zirga saboda kwantar da rigimar.

https://p.dw.com/p/3z0WR
Nigeria Soldaten
Hoto: picture-alliance/dpa

Gwamnatin jihar Filato ta sanya dokar hana zirga zirgar jama'a a tsakanin  wasu kananan hukumomi uku na jihar, sakamakon tashin hankali da ya auku a ranar Asabar.

Yankunan da dokar ta shafa dai su ne; Jos ta Arewa da Bassa da kuma Jos ta kudu. Dokar za kuma ta fara aiki ne daga karfe shida na yammaci zuwa karfe shida na safiya.

Wata sanarwa da gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya sanya wa hannu, ta ce an dauki matakin ne sakamakon yadda hankulan al'umma suka tashi bayan kisan wasu matafiya Musulmai akalla 30 a Safiyar Asabar yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kudancin Najeriya.

Sanarwa ta gwamnatin jiha ta Filato ta ce jamai'an tsaro na kokari wajen ganin an zakulo wadanda ke da hannu wajen aikata kisan, sannan ta yi Allah wadai da irin halin da jihar Filato ta shiga na bakin ciki saboda faruwar lamarin.