1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nada Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano

Nasir Salisu Zango MNA
March 9, 2020

Bayan da gwamnatin jihar Kano da ake arewacin Najeriya ta tube Sarki Muhammadu Sanusi II, yanzu haka an nada Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano.

https://p.dw.com/p/3Z65j
Emirs-Palast in Kano
Hoto: Tanja Suttor-Ba

A wannan Litinin an wayi gari a Kano da wasu gungun 'yan banga girke a kusa da fadar Sarki, sai kuma gefe guda da aka zube 'yan sanda da makamai a bakin shiga fadar masarautar. Can kuwa daga majalisar dokokin jihar rikici ne ya turnuke a tsakanin 'yan majalisar dangane da yunkurin yin dokar da za ta bai wa gwamna damar tube sarkin. Haka kuma rahotanni sun nuna cewar majalisar zartaswar jihar ta kira wani taron gaggawa, wanda shi ma ake alakanta shi da wannan batu.

Tun daren ranar Lahadi labarai ke ta yaduwa na cewar a ranar Litinin din nan gwamnatin Kano za ta zartas da kudirin ta na tube sarki Muhammad Sanusi II daga kan mukaminsa na Sarkin Kano. An dade dai ana tsallen bakade a tsakanin gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje da kuma Sarkin, tun bayan da tsagin gwamnati ya zargi Sarkin da yin kalaman da suka fusata gwamnati da kuma zargin shiga siyasa a zaben 2019 da ya gabata.

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar GandujeHoto: Salihi Tanko Yakasai

An dade ana bin matakai na kokarin kaiwa ga tube Sarkin har ta kai wannan yunkuri ya ta samma zama barazana ga tsaro a Kano lamarin da ya sa wani kwamiti karkashin tsohon shugaban Najeriya Janar Abdusalam Abubakar bisa sahalewar fadar shugaban kasa ya tsoma baki.

Su ma 'ya'yan kungiyar dattawan arewa sun yi nasu yunkurin na sasantawa amma duk bai haifar da sakamako mai kyau ba. Daga bisani ne kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta sake dauko batun bincike a kan Sarkin dangane da wani gandun Sarki da ake zargin an sayar. Sai kuma batun kwanan nan wanda aka jiyo wasu mutane daga yankin Ja'en a karamar hukumar Gwale da suka kai korafi majalisar suna neman a cire Sarki saboda dalilan saba al'ada da addini.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da gwamnatin jihar ta sauke
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da gwamnatin jihar ta saukeHoto: Getty Images/AFP/A. Abubakar

Yanzu dai an yi ta mai dungurumgum wai haihuwa da hanji, domin bayan da wadancan biye-biye da zagaye-zagaye suka gaza bullewa, gwamnatin Kano ta tube Sarki Muhammadu Sanusi II. Sakataren gwamnatin jihar Kano Alhaji Usman Alhaji ne ya karanta jawabin aiwatar da wannan kudiri yana mai cewar ana zargin Sarkin da raina gwamnati da sauran hukumomi.

Mutane da dama na bayyana ra'ayinsu a kan wannan mataki suna masu cewar an ta samma rusa tsarin sarauta a Kano.

Zuwa yanzu dai an girke 'yan sanda da dama da 'yan tauri a kofar fadar masarautar Kano. Tun fako ma dai akwai hasashe da yawa a kan Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero da dan uwansa na haihuwa Nasir Ado na cikin wadanda ke neman kujerar. Amma yanzu gwamnatin jihar ta nada Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kanon.