1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Atiku ya samu tikitin yin takara a PDP

May 29, 2022

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP, ta zabi tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar a matsayin wanda zai tsaya mata takarar shugabancin kasa a zaben 2023 da ke tafe.

https://p.dw.com/p/4C0Qb
Najeriya I Atiku Abubakar I Dan Takarar Shugaban Kasa I PDP
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku AbubakarHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP

Wannan dai na nufin tsohon mataimakin shugaban Najeriyar Atiku Abubakar din, ake fatan ya gaji shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari. Mai shekaru 75 a duniya, Abubakar yasha kaye a hannu Buhari da a yanzu haka yake kammala shekaru takwas a kan karagar mulki lokacin da aka zabe shi a wa'adi na biyu a zaben da ya gabata na shekara ta 2019. Jam'iyyar PDP din dai ta kwashe shekaru 16 tana mulki a Najeriya, kafin jam'iyyaar APC ta Shugaba Buhari ta karbe iko shekaru bakwai din da asuka gabata a yayin zaben shekara ta 2015.
Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya David Mark ne ya bayyana tsohon mataimakin shugaban Najeriyar Atiku Abubakar a matsayin dan takara na jam'iyyar PDP ta adawa a zaben na badi. Abubakar din dai ya samu kuri'u dai-dai har 371 wajen doke abokan takararsa 11 a wata fafatawa mai zafi da ta dauki hankali cikin Najeriyar da ma a wajenta. Gwamnan Rivers Nyesom Wike ne dai yazo na biyu da kuri'u 237 a yayin kuma da Abubakar Bukola Saraki ya zo na uku bayan da ya samu kuri'u 70. Wannan matakin na PDP dai, ya kawo karshen tsarin karba-karba da jam'iyyar ta yi amanna da shi a baya. Sai dai ba duka ne suka yi farin ciki da sakamkon zaben ba, inda magoya bayan gwamnan Rivers Nyesom Wike ke yin korafin da ma sun san za a rina.

Najeriya | PDP I Zaben Fitar da Gwani I Shugaban Kasa
Atiku ya lashe zaben fitar da gwani a Jam'iyyar PDP mai adawa a NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW