1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: NLC ta yi watsi da karin farashin mai

Uwais Abubakar Idris ATB
August 15, 2023

A Najeriya kungiyar kwadagon kasar ta bayyana adawa da karin farashin man fetur da wasu ‘yan kasuwa suka fara aiwatarwa a wasu jihohin kasar sakamakon tashin farashin kudin Dalar Amurka

https://p.dw.com/p/4VD6X
Nigeria Tankstelle in Abuja
Hoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Sake fuskantar karin farashin man fetur a Najeriya karo na uku a kasa da watani uku tun bayan janye tallafin mai da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi ya haifar da damuwa a tsakanin ‘yan Najeriya. ‘Yan kasuwar man fetur masu zaman kansu a Najeriyar sun bayyana cewa farashin kowace litar man fetur zai iya kaiwa tsakanin Naira 680 zuwa Naira 720 sabanin Naira 617 a cewar mallam Abubakar Mai gandi shine mataimakin shugaban kungiyar ‘yan kasuwa masu zaman kansu ta Najeriya.

Layin mai a Abuja
Hoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Baynai sun nuna cewa an samu karin farashin mai da kashi 37.4 cikin dari a wata guda inda a  wasu sassan Najeriya aka samu karin farashin man, a biranen Maiduguri da Ibadin da ma wasu sasassan jihar Lagos. Gidajen mai masu zaman kansu ne suka yi karin da ya kai Naira 690 kowace lita. Tuni kungiyar kwadagon Najeriyar ta bayyana adawa da duk wani karin kudin man, inda ta ce kan za ta shiga yajin aiki kamar yadda Comrade Nasiru Kabir sakatren tsare-tsare na kungiyar ya baiyana.

Zanga zangar 'yan kungiyar kwadago NLC a Abuja
Hoto: Uwais/DW

Barin kasuwa ta yi halin kanta a harkar man Najeriyar dai ba sabon abu ba ne ga ‘yan kasar wadanda karin ke shafar rayuwarsu ta yau da kullum. Da alamun ‘yan Najeriya za su ci gaba da fuskantar karin kudin man fetur a kasar har zuwa lokacin da gwamnati za ta shawo kan tashin farashin dallar Amurka ko kuma ta gyara matatun man kasar da suka zama tamkar mushen gizaka.