1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Karin albashi ya bar baya da kura

Uwais Abubakar Idris
April 25, 2023

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara aiwatar da karin albashi na kashi 40 cikin 100 ga ma'aikatanta, sai dai ba ta sanya malaman jamio'i da kuma likitoci a cikin karin ba

https://p.dw.com/p/4QXcC
Nigeria Änderung der Wähung Naira
Hoto: Ubale Musa/DW

Murna da farin ciki sun cika zukatan mafi yawan ma'aikatan gwamnatin tarayya inda gwamnatin ta fara biyansu karin alawus na kashi 40 cikin 100 da ta yi alkawari. Ma'aikatan sun bayyana cewa kudin sun shiga asusu lakadan ba ajalan ba. 

Dama dai kungiyar kwadagon Najeriyar ce ta matsa a kan karin albashin wanda ta yi ta kai ruwa rana da gwamnati. Kasancewa wannan karin bai shafi Malaman jami'oin gwamnatin Najeriyar ba da likitroci ya sanya mamaki a daukacin tsarin da ake tafiya tare a cewar Comrade Nasiru Kabir sakataren tsare-tsaren kungiyar kwadagon Najeriyar.

Tsame wadannan bagarori gida biyu da suke muhimmai a karin albashin babban al'amari ne a yadda ake tafiya yanzu a kan harkar albashi a Najeriyar, saboda a lokutan baya sun sha yajin aiki tare a kan kyautata masu yanayin aiki. 

Gwamnatin dai ta yi gum a kan dalilanta na cire malaman jamio'I da likitoci a kan wannan kari. Tuni shugaban kungiyar malaman jamioin Najeriyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya yi gargadin illar da wannan zai iya haifarawa.