1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ISWAP ta rasa shugaba a Najeriya

October 14, 2021

A karon farko cikin tsawon wata guda, rundunar tsaron Tarayyar Najeriya ta tabbatar da mutuwar shugaban kungiyar ISWAP ta ta'adda, Abu Musab al-Barnawi.

https://p.dw.com/p/41hQ7
Nigeria Soldaten patrouillieren in Tungushe
Hoto: AFP/Str

Cikin watan Satumbar da ya gabata ne dai, majiyoyi suka bayar da labarin kisan Abu Musab al-Barnawi shugaban kungiyar 'yan ta'addan IS reshen Afirka ta yamma wato ISWAP. Kafafen labaran Najeriyar dai sun yi baki biyu, dangane da musabbabin mutuwar al-Barnawi da ta zo kasa da watanni uku da kisan abokin hammayarsa Abubakar Shekau jagoran kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram. Rundunar tsaron Najeriyar dai, ta tabbatar da kisan Albarnawin duk da cewar ba ta ce ita ce ta halaka shi ba.

Tsohon shugaban Boko Hara Abubakar Shekau
ISWAP ce ta sanar da cewa ta halaka tsohon shugaban Boko Hara Abubakar ShekauHoto: picture-alliance/AP Photo

Babban hafsan tsaron kasar Janar Lucky Irabor ya ce lallai al-Barnawi ya tafi barzahu. Cikin wani jawabi na kasa da dakika 15 ga manema labarai ne dai, Janar Irabor ya tabbatar da mutuwar da ke zaman mai tasiri a kokarin kai karshen ayyukan 'yan ta'addan da suka addabi Najeriyar da makwabtanta. Duk da cewar babu tabbaci har ya zuwa yanzu daga kungiyar ISWAP din da al-Barnawi ke jagoranta, tabbacin mutuwar a bangaren jami'an tsaron Najeriyar na iya sauya matakai dama na kokari na kai karshen rikicin da ya haura shekaru 12. Kabir Adamu mai sharhi ne kan al'amuran tsaro a Najeriya, kuma acewarsa duk da rudanin da ke akwai da ma rashin isassun shaidu sanarwar mutuwar na iya tasiri a kokarin kare yakin da ke zaman mafi dadewa a kasar.

Mayakan Boko Haram
Mayakan Boko Haram sun jima sun cin karensu babu babbaka a Najeriya da makwabtaHoto: picture alliance/AP Photo

Sama da 'yan kungiyar dubu 13 ne da iyalansu dai, rundunar tsaron ta ce sun mika wuya tun bayan kisan shugabannin kungiyoyin biyu. A watan Yunin da ya gabata ne dai, aka tabbatar da labarin kisan Shekau da ya nemi zama mai rai guda tara. To sai dai kuma in har sojan na tsallen mura a yankin Arewa maso Gabas, can ma a dan uwansa na Yamma sojojin sun ce suna samun nasara a kokarin tunkarar barayin dajin yankin. Kuma Janar Irabor ya ce ya zuwa Litinin din wannan makon, sama da barayin 250 suka hallaka ko bayan wasu 600 da suka shiga hannu tun bayan toshe kafofin sadarwa makonni shidan da suka gabata. Nasara a bangaren mahukuntan dai, na zaman kwarin gwiwa cikin kasar da ke dada fuskantar zabe amma kuma ke kallon barazanar kasa zuwa yakin.