1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Najeriya kan gargadin Amurka

Uwais Abubakar Idris
November 7, 2023

Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani a kan gargadi da Amurka ta yi na barazanar hari a otel-otel da ke manyan biranen kasar saboda rashin tsaro da ake fama da shi.

https://p.dw.com/p/4YW9b
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Emmanuel Osodi/AP Photo/picture alliance

Jan hankali da kuma gargadin yin taka tsan-tsan da kasar Amurkan ta yi ga masu ziyara da gudanar da harkokinsu a Najeriya musamman ‘yan kasarta, wanda ofishin jakadancin Amurkan da ke Najeriya ya ce yana da sahihan bayanai da suka tabbatar da barazanar a kan otel otel a manyan biranen Najeriyar. Wannan dai kara daga batun ne da ma bashi karfi bisa ga wanda Amurikan ta yi a baya a cewar Dr Kabiru Adamu shugaban cibiyar Beacon da ke aiki a fanin tsaro a Najeriyar.

Anthony Blinken sakataren harkokin wajen Amurka
Anthony Blinken sakataren harkokin wajen AmurkaHoto: Jonathan Ernst/Reuters/AP/picture alliance

A baya dai barazana irin wannan ta tada kura sosai a Najeriya, inda ra'ayoyi kan sha bamban a kan yadda Amurkan ke fitar da irin wannan gargadi kan barazanar da take dangantawa da rashin tsaro. Da alamu a wannan karon abin ya taba gwamnatin Najeriyar da ta kai ga mayar da martani a kan illar da take gani kan wannan sanarwa kamar yadda ministan yada labaran Najeriya Alhaji Mohammed Idris ya nunar.

Hoton birnin Maiduguri daga sama
Hoton birnin Maiduguri daga samaHoto: Mark Naftalin/EPA/UNICEF/dpa/picture alliance

A kwanakin baya hukumomin tsaron Najeriya sun bankado yunkurin kai hare-hare a biranen Minna da ke jihar Niger da birnin Kano inda ta kama makamai masu yawa, baya ga nasarar murkushe ‘yan ta'addar. Sai dai an fuskanci wasu munana hare-hare a Maiduguri da Katsina. 

Ra'ayoyi dai sun shan bamban a kan irin wannan gargadi da Amurikan kan fitar na barazanar ta tsaro.