1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun koli ta bai wa Ganduje nasara

Nasir Salisu Zango RGB
May 6, 2022

Kotun kolin Najeriya ta yanke hukunci kan dambarwar da ake yi a game da shugabancin jam'iyyar APC na Kano inda ta bai wa Gwamna Abdullahi Ganduje nasara.

https://p.dw.com/p/4AwuK
Nigeria Wahlkampf von APC-Partei in Kano
Hoto: Salihi Tanko Yakasai

A jihar Kano mutane na ci gaba da yin martani a dangane da hukuncin kotun kolin Najeriya wacce ta kori karar da tsagin G7 na jam'iyyar APC a Kano suka shigar suna kalubalantar shugabancin jamiyyar da ke karkashin Abdullahi Abbas da gwamna Umar Abdullahi Ganduje ke marawa baya, sai dai kuma tsagin na G7 sun ce da sauran ruwa a kaba domin kuwa sun sake garzayawa kotun inda suka sake shigar da sabuwar kara lamarin da ke jawo kace-nace a kano.

Karin Bayani:Najeriya: Rikici ya mamaye zaben Kano

Hukuncin kotun kolin wacce akewa lakabi da kotun daga ke sai Allah ya isa, bai yi wa 'yan jam'iyyar APC tsagin G7 dadi ba la’akari da yadda hukuncin yayi musu tumbur tare da jefa su cikin wani irin haki na katankatana wai mutuwar bakin al’muru.

Barista Abdul Fagge shi ne mai bai wa jam'iyyar APC shawara a fannin shari'a ya ce, aikin gama ya gama domin kotu tayi hukunci dan haka yake kira 'yan tsagin G7 da su zo a hade domin samun nasarar jam'iyyar APC a Kano.

Karin Bayani:Kwankwaso da Ganduje: Ko za a yi sulhu?

Da alama a iya cewar da sauran rina a kaba domin kuwa Ahmadu Haruna Zago, wanda shi ne hukuncin ya yi wa tutsu ya ce, bayan tiya akwai wata cacar, domin ya sake komawa babbar kotun tarayya da ke Kano domin shigar da sabuwar kara, dan kalubalantar shugabancin Abdullahi Abbas.

To amma ga dattijan tsagin G7 irin su Alhaji Shehu Dalhatu hukuncin bai ba su mamaki ba, kuma fafutukar da suke ta kokarin dawo da siyasar Kano cikin hayyacinta ne, dan haka za su duba matakin da za su dauka. Sai dai kuma gabanin wannan hukunci an fara samun tangarda a kunshin tsagin G7 bayan da aka fara zaman sulhu tsakanin jagoran tawagar Malam Ibrahim Shekarau da gwamna Ganduje, har ma na hannun daman Malam Shekarau Alhaji Yakubu Yarima ke cewar dama can babu rikici tsakanin shekarau da Gandujen.