1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahaman Ousmane bai amince da kaye ba

Gazali Abdou Tasawa LMJ
March 23, 2021

A Jamhuriyar Nijar dan takarar adawa Alhaji Mahaman Ousmane ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa zagaye na biyu, wanda kotun tsarin mulkin kasar ta ayyana a Bazoum Mohamed a matsayin wanda ya lashe.

https://p.dw.com/p/3r0nl
Mahamane Ousman Ex-Präsident Niger
Dan takarar jam'iyyar adawa a Jamhuriyar Nijar Mahamane OusmanHoto: DW/M. Kanta

Alhaji Mahaman Ousmane ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira a daren Litinin din da ta gabata, inda ya yi kira ga magoya bayansa da su fita zanga-zanga a duk fadin kasar domin nuna rashin amincewarsu da abin da ya kira kwace masa nasarar zabe. Daruruwan magoya bayan jam'iyyun adawa ne dai suka bukaci ya fito ya ce wani abu a kan sakamakon da kotun tsarin mulki ta bayyana, hasalima wasunsu sun bayyana cewa ba shi da wani zabi illa ya ce bai amince da sakamakon ba kana ya bukaci su fito su yi zanga-zanga.

Karin Bayani:Zan yi aiki da kowa don gina kasa - Bazoum

Bayan wata doguwar tattaunawa ta kusan tsawon yini guda tare da sauran shugabnnin adawa Alhaji Mahaman Ousmane ya fitar da sanarwar, inda ya nuna rashin amincewarsa da sakamakon zaben da kotun tsarin mulkin ta bayyana yana mai zargin ta bayyana sakamakon ba tare da lura da korafe-korafen da ya shigar a gabanta ba.

Verfassungsgericht in Niamey Niger
Kotun tsarin mulki ta Jamhuriyar NijarHoto: DW/M. Kanta

Dan takarar adawar ya kuma yi kira ga sojoji da sauran jami'an tsaro cewa kamar yadda doka ta tanada, bai zamo dole su yi biyayya ga umurnin da ake bayar wa ba kan ka'ida ba, musamman daga abin da ya kira haramtacciyar gwamnatin Nijar. Sai dai da take mayar da martini, jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya ta bakin daya daga cikin kusoshinta Honourable Kalla Moutari ta ce, kalaman dan takarar adawar ba su zo masu da mamaki ba.

Karin Bayani: An katse kafar internet a Jamhuriyar Nijar

Yanzu dai za a iya cewa Mahaman Ousmane na cikin halin tsaka mai wuya, na neman kare mutuncinsa da akidarsa ta neman zaman lafiya da kuma bukatar wasu daga cikin jam'iyyun da ke mara masa baya na ganin ya saka kafar wando guda da hukuncin kotun tsarin mulkin. Sai dai kuma kawo yanzu kiran zanga-zangar da Ousmane ya yi ga 'yan kasa bai soma yin tasiri ba a birnin Yamai, inda lamurra ke tafiya kamar kullum a yayin da jami'an tsaro a cikin damara suka ja daga a wurare da dama wasu kuma na sintiri da motocinsu a kan titunan birnin na Yamai.