1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba ta sauya ba a kan iyakokin Nijar

February 26, 2024

Ga dukkan alamu babu wani sauyi daga al'amuran zirga-zirga na shige da fice a kan iyakokin Jamhuriyar Nijar da Benin da ma Najeriya, duk kuwa da dage takunkuman da kungiyar ECOWAS CEDEAO tayi.

https://p.dw.com/p/4cuUD
Nijar | Benin | Najeriya | Kan Iyaka
Har yanazu zirga-zirga ba ta dawo yadda ya kamata ba a kan iyakokin NijarHoto: Mohammed Babangida/AP/dpa/picture alliance

Bayan da shugabannin kasashe mambobin kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO suka sanar da janye wani bangare na takunkumin da suka kakabawa Jamhuriyar Nijar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar, wwadanda suka hadar da bude kan iyakokin kasashe mambobin kungiyar da ke makwabta da Nijar 'yan kasar mazauna kan iyakokin Bénin Nijar din da kuma Najeriya suka shiga nuna murnarsu. To sai dai kwana biyu da wannan sanarwar babu wani sauyi a kan iyakokin, hasali ma dai dakarun sojojin Nijar da aka jibge a kan iyakokin na cikin shirin ko ta kwana. Daga bangaren gwamnatin kasar Nijar kuwa, har kawo yanzu ba su ce uffan ba.

Njar | Sojoji | Benin | Najeriya
Tun bayan juyin mulkin soja, aka shiga takaddama tsakanin Nijar da makwabtantaHoto: AFP

Moussa Amadou Modibo wani mai sharhi ne a kan harkokin yau da kullum, ya ce dole ne gwamnatin kasar ta yi taka-tsan-tsan da makwabtan nata na Benin da Najeriya. Hadiza wata 'yar kasuwa a tashar jirgin ruwa ta ce, fatan 'yan kasuwa shi ne shugabannin su yi iyakar bakin kokarinsu domin ganin an samu jituwa a tsakanin kasashen da ke makwabtaka da juna. A ra'ayin Attiku Dotti wani mai sharhin kuwa, har yanzu da sauran rina a kaba idan har za a sasanta matsalar da ke tsakanin ECOWAS ko CEDEAO  da kuma Jamhuriyar Nijar. Shi kuwa dan kasuwa Elhadj Issifou Hayyatou cewa ya yi, akwai bukatar gwamnatin Nijar din ta dubi talakawa da idon rahama. 'Yan kasa dai na ci gaba da zurawa gwamnati idanu, domin ganin irin matakin da za ta dauka a tsakanin bude nata iyakokin ko kuma ci gaba da rufe su.