1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta kulla yarjejeniyar tsaro da Rasha

Abdoulaye Mamane Amadou ZMA
January 17, 2024

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta kulla yarjejeniyar tsaro da kasar Rasha, a albarkacin wata ziyarar aiki da tawagar jagororin kasar suka kai a birnin Moascow.

https://p.dw.com/p/4bLf7
Firaministan Nijar  Ali Mahaman Lamine Zeine
Firaministan Nijar Ali Mahaman Lamine ZeineHoto: DW

Gwamnatin Rasha ta cimma yarjejeniyar kara karfafa huldarta ta fannin tsaro da Jamhuriyar Nijar, hukumomin Moscow, sun ce a yayin wata ganawarsu da firaministan rikon kwaryar Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine da mukarabansa, sun kulla yarjejeniyar tsaro da kara inganta hulda ta fannonin ci gaba da dama a tsakanin kasashen biyu.

Karin Bayani :  Nijar: Sabon babin hulda da manyan kasashe

Tun da jimawa Moscow ke fatan fadada komarta a wasu yankunan yammacin Afirka, ciki har da Jamhuriyar Nijar da sojoji suka kifar da gwamnatin dimukuradiyya a cikin watan Yulin 2023, tare da daukar matakan korar dakarun Faransa daga kasar a karshen shekarar 2023, matakin da ya kai jami'an gwamnatin Rasha ziyara a Nijar a cikin watan Dismaban 2023.

Karin Bayani :  Nijar: Ziyarar jami'an gwamnatin Rasha

Tawagar ta Jamhuriyar Nijar da ke rangadin za ta ci gaba zuwa wasu kasashe, ciki har da Turkiya da Iran, bayan da ta yada zango a birnin Moscow.