1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarki Charles na III na kammala ziyara a Jamus

March 31, 2023

Sarki Charles na III na Birtaniya tare da mai dakinsa Camilla za su kammala ziyarar kwanaki uku da suke yi a nan Jamus inda za su kammala da ziyara a birnin Hamburg.

https://p.dw.com/p/4PX44
Hoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Manyan bakin na alfarma, za su yi amfani ne da jirgin kasa na Deutsche Bahn mallakin Jamus tare da shugaban kasa Frank-Walter Steinmeier da mai dakinsa shi ma Elke Büdenbender da suka fito daga Berlin.

An dai tsara wata liyafa ta musamman a ofishin magajin garin birnin na Hamburg sannan za a zagaya da Sarkin na Birtaniya cikin birnin.

Zai kuma ziyarci wajen tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a lokacin yakin duniya na biyu, kafin a daga bisani Sarki Cahrles na III ya karkare da ziyara zuwa ofishin jakadancin Birtaniya da ke a Hamburg din.