1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Yanayi

Bankin Duniya: Illar sauyin yanayi a Sahel

Salissou Boukari LMJ
September 22, 2022

Rahoton Bankin Duniya ya yi nuni ga Jamhuriyar Nijar da sauran makwabtanta na yankin Sahel, dangane da yadda matsalar sauyin yanayi ka iya haddasa karuwar talauci a kasar muddin dai ba a dauki matakan da suka dace ba.

https://p.dw.com/p/4HES0
Senegal | Yaki | Hamada | Dashe | Bishiyoyi | Green Wall
Shirin yaki da kwararowar hamada na Green Wall a yankin SahelHoto: Zohra Bensemra/Reuters

Rahoton dai ya tabbatar da cewa radadin sauyin yanayi na shafar al'umma sosai, ta yadda yake dakushe irin kokarin da kasashe ke yi a fannin ci gabansu. Kuma nazarin ya nunar cewa sauyin yanayi ka iya ta'azzara matsalar talauci nan da shekara mai zuwa, muddin ba a dauki matakai kwarara a kasashen yankin na Sahel kamar Jamhuriyar Nijar ba. A cewar mataimakin shugaban Bankin Duniya mai kula da kasashen yammacin da tsakiyar Afirka, bincike ya nunar da cewa al'ummar yankin na sahel za ta rubunya sau biyu nan zuwa shekaru 20 masu zuwa. Ya nunar da cewa, a yankin na Sahel kadai yawan al'umma zai kai miliyan 160. Lokaci zuwa lokaci dai gwamnati da sauran wakilan al'umma zababbu, na shiga cikin karkara domin ganin halin da ake ciki.

Sahel | Niger I Agadez | Hijira | Yawan Al'umma
Dubban mutane ne dai, ke yin kaura daga yankin na Sahel Hoto: Kristin Palitza/dpa/picture alliance

'Yan majalisar dokoki da dama sun yi rangadi a cikin karkara, domin ganewa idanunsu yadda lamura ke gudana dangane da matakan fuskantar matsalolin yaki da talauci da sauyin yanayin. Rahoton ya tabo batun kariyar muhalli musamman ma batun kiyaye saran itace da ke janyo kwararowar hamada. Sai dai kuma a cewar Hon Mu'azou Tchangalla dan majalisar dokoki na Jamhuriyar Nijar, wata hanya mafi dacewa ita ce ta amfani da isakar gas birni da kauye wajen girki domin rage sare dazuzzuka. Rahoton na Bankin Duniya dai ya ce akwai shawarwari da ya kamata kasashen su yi amfani da su, ta yadda za su samu hanyoyin bunkasa tattalin arzikinsu da samar da sauye-sauye musamman ma a fannin yaki da kwararowar hamada tare da farfado da wuraran noma da suka riga suka zaizaiye. Hakan zai bai wa al'ummar karkara damar bayar da himma, wajen aikin noma tukuru tare da dashen itatuwa.