1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukukuwan Kirsimeti na 2022

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 22, 2022

Mabiya addnin Kirista a fadin duniya na gudanar da bukukuwan Kirsimeti da suka saba gudanarwa duk shekara, a wani mataki na tunawa da Yesu Al-masihu.

https://p.dw.com/p/4LL9l
Kirsimeti | Kiristoci | Kyauta | Biki
Bayar da kyaututtuka yayin bukukuwan KirsimetiHoto: Lyu Tianran/Xinhua/picture alliance

A duk shekara mabiya addinin Kirista a fadin duniya, kan gudanar da shagulgulan bikin na Kirsimeti domin tunawa da ranar da suka hakikance a ita aka haifi Annabi Isa (A.S). Yayin wannan biki, su kan gudanar da addu'o'i da ziyarar 'yan uwa da abokan arziki har ma da raba kyaututtuka domin karfafa zumunci.

Duk da cewa a kan koka da tsadar rayuwa a irin wadannan lokuta na gudanar da bukukuwa, hakan baya hana mabiya addinin Kirista din yin bikin tunawa da Yesu Al-masihun. A wasu yankunan na kasashen Afirka kamar Najeriya, al'ummar Musulmi kan taya 'yan uwansu Kiristoci murna ta hanyar ziyartar su da ma kai musu tallafi da kyaututtuka.

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna

Rahotanni da Sharhuna