1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojan Somalia ya harbe abokanan aikinsa 5

Binta Aliyu Zurmi
February 11, 2024

Sojan Somalia ya bude wuta a sansanin sojoji da ke birnin Mogasihu yayin atisaye, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji biyar, 4 hHaddadiyar Daular Larabawa da wani guda na kasar Baharain.

https://p.dw.com/p/4cGtQ
Somalia Sicherheitskräfte in Mogadischu
Hoto: Abukar Muhudin/AA/picture alliance

Sojan wanda rahotanni ke cewar ya bude wutar ne a yayin da sojojin ke salla, sai dai nan take aka harbe shi a wani mataki na kariya.

Ya zuwa yanzu babu masaniya a kan dalilan kai wannan harin da sojan ya yi a kan abokan aikinsa, sai dai tuni kungiya kungiyar Al-shabab da ke gwagwarmaya da makamai wacce kuma ke da alaka da da kungiyar Al-Qaeda da ta jima tana kadammar da hare-hare a kan jami'an gwamnati sama da shekaru 15 ta dauki alhakin harin.

Mahukunta a Hadaddiyar Daular Larabawa sun yi Allah wadai da harin, tun a shekarar 2023 Kasashen Somalia da Haddadiyar daular Larabawa suka kulla yarjejeniyar samar da tsaro.