1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Sojojin Isra'ila sun yi wa Gaza kawanya

October 9, 2023

Isra'ila na ci gaba da kai wa Gaza hare-hare ta sama bayan yi wa yankin kawanya

https://p.dw.com/p/4XJWm
Barin wuta ta sama a zirin Gaza
Barin wuta ta sama a zirin GazaHoto: Mahmud Hams/AFP

Hukumomin Isra'ila sun bayar da umarnin datse hanyar bayar da ruwan sha ga yankin Gaza nan take, a daidai lokacin da suke ci gaba da luguden wuta ta sama kan yankin na Falasdinawa.

Ministan lantarki ne ya bayar da wannan umarnin na gaggawa, jim kadan bayan da ministan tsaro Yoav Gallant ya bayar da umarnin yi wa Gaza kawanya.

Kashi 10 cikin 100 na ruwan sha da ke zuwa Gaza, yana fitowa ne daga Isra'ila.