1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Steinmeier ya nemi daukin Xi a yakin Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
December 20, 2022

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi kira ga shugaban kasar Chaina Xi Jinping da ya yi amfani da tasirinsa kan Vladimir Putin wajen kawo karshen yakin da ake yi a Ukraine.

https://p.dw.com/p/4LFSY
Bundespräsident Frank-Walter Steinmeier | Treffen mit iranischstämmigen Menschen
Hoto: Britta Pedersen/dpa/picture alliance

A cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Berlin, Shugaba Frank-Walter Steinmeier na Jamus ya nunar da cewa ya tattauna da shugaban kasar Sin Xi Jinping ta wayar tarho, inda ya jaddada moriyar da Sin da Turai za su ci idan aka kawo karshen yakin. Wannan tattaunawar da ta dauki mintuna 60 tsakanin shugabannin biyu, ta kuma mai da hankali kan "dangantakar da ke tsakanin Jamus da Chaina.

Tun lokacin da aka fara yaki a kasar Ukraine, kasashen yammacin duniya ke ta kokarin yin matsin lamba kan kasar Chaina, saboda kusanci da take da shi da Rasha. Sai dai a yayin ziyarar da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya kai kasar Chaina a baya-bayan nan,  Shugaba Xi Jinping ya nuna rashin amincewarsa da karuwar makaman nukiliya a yakin Ukraine.