1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tuhumi Trump a Jihar Georgia.

Abdourahamane Hassane
August 15, 2023

Wani alkali a Atlanta ya yanke hukuncin cewa Trump zai gurfana a gaban kuliya saboda yunkurin da ya yi na yin tasiri a sakamakon zaben shugaban kasa na jihar a shekara ta 2020 wanda ya yi ikirarin lashewa.

https://p.dw.com/p/4VAGJ
Donald Trump tsohon shugaban Kasar Amirka
Donald Trump tsohon shugaban Kasar AmirkaHoto: Alex Brandon/AP Photo/picture alliance

Wannan dai shi ne tuhume-tuhume na hudu da ake yi wa Donald Trump mai shekaru 77 da haihuwa, kana na biyu da ya shafi zaben shugaban kasa na shekara ta 2020. Haka kuma za a  gurfanar da wasu mutane 18 da ake tuhuma da suka hada da tsohon shugaban ma'aikatan fadar White House Mark Meadows da tsohon lauyan Trump Rudy Giuliani.