1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra’ila da Hamas sun cimma yarjejeniya

Zainab Mohammed Abubakar
November 22, 2023

Isra’ila da Hamas sun cimma matsaya kan tsagaita wuta don gudanar da aiyukan jin kai na tsawon kwanaki hudu, inda a madadinsa za a saki 50 daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.

https://p.dw.com/p/4ZI4q
Hoto: Rizek Abdeljawad/Xinhua News Agency/picture alliance

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta ce za a sanar da lokacin da sojojin Isra'ila za su dakatar da kai harin cikin sa'o'i 24 masu zuwa.

Yarjejeniyar ta hada da sakin fararen hula mata da kananan yara 50 da ake garkuwa da su aGaza, a yayin za a sako wasu mata da kananan yara Falasdinawa da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila, kuma za a kara adadin wadanda za a saki a mataki na gaba na aiwatar da wannan yarjejeniyar.

Tsawon makwanni kenan, Qatar ta matsa kaimi wajen tattaunawarshiga tsakani ta bayan fage, da nufin kubutar da wasu daga cikin mutane 240 da aka yi garkuwa da su a Gaza, domin neman tsagaita wuta na wucin gadi da kuma samun damar kai kayan jin kai cikin wannan yanki da yaki ya daidaita.

A ranar 7 ga watan Oktoba ne 'yan bindigar Hamas suka kai farmaki ta kan iyakar Gaza da ake tsaro dare da rana, harin da ke zama mafi muni a tarihin Isra'ila.