1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine ta koka kan jinkirin zuwan tallafin ketare

February 20, 2024

Shugaban Ukraine ya ce sojojin Rasha na samun galaba a sabili da jinkirin da ake samu wajen tallafa wa Ukraine, yana mai nuna yadda rashin makamai ke ci gaba da dakile kokarin da ya ce dakarun nasa na yi.

https://p.dw.com/p/4cb8E
Hoto: Johannes Simon/Getty Imag

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya koka kan hali na kunci da ya ce dakarun kasar da ke fagen daga ke ciki. A wata ziyara da ya kai wa sojojin kasar a yankin Kharkiv, Zelenskyy, ya ce rashin isowar tallafin da kasashen Yammasuka alkawarta wa Ukraine ya jefa dakarunsu cikin mawuyacin halin.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da aka samu rabuwar kai a tsakanin majalisar dattawan Amurka da kuma ta wakilai kan tallafin kudade biliyan 60 na Dala da Shugaba Joe Biden ke son aike wa Ukraine, yayin da sanatoci suka amince da wannan kuduri, su kuma 'yan majalisar wakilan kasar na jan kafar fara tattauna kudurin.