1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwanaki 100 na sabon shugaban Kenya

December 22, 2022

Bayan da Shugaba William Ruto na Kenya ya cika kwanaki 100 a kan karagar mulki, al'umar kasar na bayyana ra'ayoyinsu dangane da alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zabe.

https://p.dw.com/p/4LJsL
Kenya |William Ruto | Mulki | Kwana 100
Shugaba William Ruto ya yi kwanaki 100 da rantsuwar kama mulkin KenyaHoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

Daga cikin alkawuran da Shugaba William Ruto ya yi wa 'yan kasar ta Kenya dai, akwai batun rage tsadar rayuwa ta hanyar zaburar da harkokin tattalin arziki. Shugaba Ruto dai ya samu yabo daga bangaren shari'ar kasar, bayan karin girman da ya yi wa wasu manyan alkalai su shida da shugaban da ya gada Uhuru Kenyatta ya yi watsi da daga darajarsu duk da shawarar da ma'aikatar da ke kula da alkalai da ayyukan shar''a ta bayar. Shugaba Ruto ya kuma yi alkawarin aiki kafada da kafada da bangaren shari'ar domin tabbatar da wanzuwar adalci a kasar, kuma a fadar Eric Theuri shugaban kungiyar lauyoyin kasar ta Kenya bai saba alkawarin ba cikin kwanakinsa 100 a kan madafun iko. To sai dai 'yan kasar da dama musamman kungiyoyin kare hakkin dan Adam, na dari-dari da majalisar ministoci da ma bangaren shari'ar.

Kenya | William Ruto | Kwanaki 100 | Shari'a | Ci-gaba | kotun Koli
Bangaren shari'ar Kenaya ya samu ci-gaba, a kwanaki 100 na mulkin William Ruto Hoto: Yasuyoshi Chiba/AFP

Baya ga fannin na shari'a dai Shugaba Ruto ya yi alkawarin rage tsadar rayuwa tare da samar da jari ga matasa, alkawuran da wadanda abin ya shafa suka ce sam bai cika su ba. Sai dai kuma ra'ayoyi sun sha bam-bam a bangaren masana da masharhanta, inda Farfesa Fred Ogola kwararre ne a kan harkokin tafiyar da gwamnati ke cewa Shugaba Ruto bai burge shi ba a kwanaki 100 da ya yi a karagar mulkin Kenyan. To amma ga Janet Ouko wata mai sharhi kan harkokin ilimi da shugabanci, fannin ilim dai sai san barka cikin wadannan kwanaki na Shugaba Ruto ko da yake abu ne da ke matsayin kada-ran kada-han. Shugaban dai na ci gaba da shan matsi kan yadda rayuwa ke kara tsanani ganin da bakinsa ya ce zai dauki mataki a kan matsalar. Abin da mutane ke son gani shi ne rage farashin man fetur da na kayan masarufi, amma maimakon samun hakan sai tashi suka yi musamman ma bangaren sufuri.