1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Yadda shekarar 2023 ta kasance a yankin Gabas ta Tsakiya

Kersten Knipp Abdourahmane Hassane (Abdoulaye Mamane)
December 29, 2023

Yakin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas, tun farkon watan Oktoba, ya canza yanayin siyasar Gabas ta Tsakiya har abada, ya dakatar da kusantar da aka fara tsakanin kasashen Larabawa da dama da Isra'ila.

https://p.dw.com/p/4ahqX
Wani mazaunin Bafalasdine zaune a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia a arewacin Gaza
Wani mazaunin Bafalasdine zaune a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia a arewacin GazaHoto: Mohammed Al-Masri/REUTERS

A cikin 'yan shekarun baya-baya nan, da yawa daga cikin shugabannin Larabawa sun yi sassauci ga Isra'ika wadanda suka yi ta kokarin kula hulda da ita, har ma ana tunanin fafutukar da ake yi na neman girka kasar Falasdinu na kamuwa da cikas dangane da yadda kasashen Larabawa suka yi fatali da zancen.

Daga shekarar ta 2020, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Bahrain, da Maroko har ma da Sudan sun fara kulla alaka da Isra'ila ta hanyar sanya hannu kan yarjejeniyoyin. Amma hare-haren na ranar 7 ga Oktoba, da Hamas ta kai a kasar Isra'ila, ya kawo karshen wannan yunkuri.

Jim kadan bayan fara yakin, an samu karin kasashen Larabawa da ke nuna goyon bayansu ga Gaza. Aiman ​​Safadi, shugaban diflomasiyyar Jordan, ya kira lamarin da sunan cikakken ta'addanci kan fararen hula a zirin Gaza wanda ke da hadarin dagula zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya baki daya. Ministan ya kuma yi magana game da laifukan yaki da Isra'ila ta aikata wanda ya hana isar da abinci, magunguna da mai zuwa yankin Falasdinu.

Batun yakin a yankin Gabas ta Tsakiyya ya yi fice a kanun labarun duniya, wanda kusan shi ne lamarin da ya fi daukar hankali a duniya. André Bank, kwararre a kan yankin na Gabas ta Tsakiyya a Cibiyar GIGA da ke Hamburg, ya bayyana cewa, musamman Masar da Jordan, masu iyaka da Isra'ila da yankunan Falasdinu, suna fargabar sakamakon yakin da ake yi.

Saudiyya ta karbi bakwancin taron kasashen Larabawa kan yankin Gabas ta Tsakiya
Saudiyya ta karbi bakwancin taron kasashen Larabawa kan yankin Gabas ta TsakiyaHoto: Saudi Press Agency/dpa/picture alliance

"A Masar, alal misali, an haramta zanga-zanga a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira, saboda shugaba al-Sissi da gwamnatinsa na fargabar cewa zanga-zangar goyon bayan Falasdinu za ta rikide zuwa zanga-zangar siyasa mai kama da rikicin Larabawa A Jordan. Ana iya yin zanga-zanga a wasu sassan babban birnin kasar Amman, amma ba a kan iyakar kogin Jordan ba."

Yawancin masu bincike da suka kware a kan Gabas ta Tsakiya sun yi imanin cewa muradun tattalin arziki na kasahen Larabawa ke a gabansu ba yakin ba. Johannes Becke na Jami'ar  Heidelberg dake a Jamus, yana ganin cewa, ba shakka jawaban wasu gwamnatocin Larabawa suna tafiya ne bisa ra'ayin jama'a, kuma suna adawa da gwamnatin Isra'ila, amma a zahiria a gaskiya, ba haka yake ba

 "A halin yanzu, ina da ra'ayin cewa babban taron koli na karshe na kasashen Larabawa da na musulmi an yi maganganu. Shugaban kasar Syria ya yi babar suka a kan Isra'ila haka ma da sauran kasashen Larabawa amma dai duk da haka babu wasu kasashen Larabawa da suka fito a hukumance suka tsinke hulda da Isra'ila."

Isra'ila ta kasance abokiyar hulda cinikaya da  kasashen yankin Gulf ta fuskar fasaha da mu'amalar tattalin arziki, haka kuma kyakkyawar alaka da kasar Isra'ila ta ba su damar ci gaba da kasancewa tare da Amurka da kasashen yammacin duniya wadanda ba sa son ganin tasirin Iran ya karu a yankin. Ban da haka kuma, Iran tana goyon bayan 'yan tawayen Houthi a Yemen, wadanda ke yaki da sojojin Saudiyya.

A farkon watan Disamba, Saudiyya ta kama makamai masu linzami daga Hamas, wadda ita ma Iran ke goyon bayanta, na yi zanga-zanga kaɗan, duk da haka, a cikin ƙasashen Gulf. Yawancin shugabannin Hamas tabbas suna zaune ne a Qatar, amma Masarautar na kallon dangantakarta da Israila a zahiri ba ta gushe ba.