1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaron Najeriya na cin zarafi

April 7, 2021

Kungiyar Amnesty International mai fafutukar kare hakkin dan Adam, ta zargi jami'an tsaron Najeriya da 'yan kungiyar Boko Haram da take hakkokin jama'a.

https://p.dw.com/p/3rh7W
Nigeria Proteste in Lagos
Jami'an tsaron Najeriya na take hakkin dan AdamHoto: Reuters/Str

Wannan zargi na kungiyar kare hakkin dan Adam din ta kasa da kasa wato Amnesty International, na zuwa ne a daidai lokacin da miliyoyin al'ummar Tarayyar Najeriyar ke tsallen murnar sauya shugabanci a rundunar 'yan sanda ta kasar. Kama daga 'yan Boko Haramu ya zuwa sojoji da jami'an 'yan sandan Najeriyar, kungiyar ta Amnesty ta hada tai wa wanki irin na babban bargo kan batun kare hakkin dan Adam cikin kasar. 

Karin Bayani: Rahoton Amnesty kan rikicin makiyaya a Najeriya

A wani rahoto na shekara-shekara da ta saba fitar wa dai, Amnesty ta ce akwai bukatar yin duk maiyiwuwa da nufin kai karshen cin zarafin mata da yara kanana a bangare na kungiyar da ta dauki lokaci tana kisa da ma yin fyade. To sai dai kuma ko bayan masu dinkin hular da suka rikide ya zuwa ga ta'adda, su kansu jami'an tsaron da ke neman tabbatar da zaman lafiya tsakanin al'ummar Najeriyar dai na wuce makadi cikin rawa ga batun na kare hakki na 'yan kasar a fada ta kungiyar. 

Karikatur Boko Haram
Zargin jami'an tsaron Najeriya da cin zarafin 'yan shi'a Hoto: DW/Baba

A cikin wani rahoto na kasa da kasa bisa batun kare 'yancin dan Adam dai, Amnesty ta ce babu mai dama walau a tsakanin sojojin da kungiyar ke zargi da cin zarafin 'yan shi'a, ya zuwa 'yan sandan da ke kan gaba cikin rikicin Lekki. Babu dai 'yanci na fada ko ba dadi haka kuma an tauye dama ta  gangami tsakanin al'umma, a fadar Auwal Musa  Rafsanjani da ke zaman shugaban kungiyar a Najeriyar. Koma wa zuwa ga mai duka cikin neman sauki ko kuma  kare hakkin al'umma, cin zarafin 'yan sandan ne dai alal ga misali ya kai ga zanga-zanga ta matasan da ta rikide ya zuwa rikici mai girma cikin kasar a shekarar data shude. 

Karin Bayani: Amnesty ta ce a kare hakkin dan Adam a Najeriya

To sai dai kuma a fadar Usman Alkali Baba da ke zaman sabon babban sifeton 'yan sandan kasar, ana shirin ganin daban a zamaninsa a dangantakar da ke da tasiri ga makomar Najeriyar. Sama da mutane 1,500 ne dai suka kai ga asara ta rayuwa, sakamakon kisa irin na ba gaira da ya mamaye  sassan Arewa maso Yammacin kasar da na Tsakiya. Kama daga rikici na kabila da 'yan ina da kisan dake gwada kwanji, ko bayan wasu miliyan biyun da rikicin Arewa maso Gabas na Boko ta Haram ya raba da muhalli. Abun kuma da fada ta rahoton yake bukatar kallo na basira.