1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin hanci da karbar rashawa na karuwa a Najeriya

Abdullahi Maidawa Kurgwi AH
December 8, 2023

A jajibirin ranar yaki da cin hanci ta duniya(09.12.23) 'yan Najeriya na bayyana damuwa sakamakon karuwar cin hanci da karban rashawa dake neman zama tarnaki ga cigaban kasar.

https://p.dw.com/p/4Zx5x
Hoto: picture-alliance/dpa/MAXPPP/Kyodo

 Tun dai a ranar 31 ga watan Oktobar sheakarar ta 2003  ce Majalisar Dinkin Duniya ta kebe rana ta musamman don duba  matakan yaki  da cin hanci da  karban rashawa tsakanin kasashen duniya. Inda a Najeriya bayan kafa dokokin  hukunta masu zambartar kasar biye da kafa hukumomin da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, irin su  EFCC da ICPC, batun cin  hanci da rashawa  dai kullum sai kara samun gindin zama yake.   

Cin hanci da karbar rashawa na karuwa a Najeriya duk da hukukomin yaki da cin hancin da aka girka

Hoto: Olisa Chukwumah/DW

 Tarihi dai ya nuna yadda gwamnatin da ta gabata ta yi nasarar kama manyan  jami'an gwamnatin kasar ciki har' da ministoci da tsoffin gwamnoni waddan da ta  samu da hanu dumu-dumu a harkar cin hanci da rashawa, inda wasun su ma  kotu ta zartar musu da hakuncin daurin shekaru. To amma a bisani sai gwamnatin ta sako su da sunan ahuwa. 'Yan Najeriya da dama dai na tambaya kan yadda za'a  ce shugabanin hukumomin da ke yaki da karban hanci, tare ma da masu kula  da baitil malin kasar kan fuskanci shari'a a gaban kotuna sakamakon zargin  cin   hanci.

Najeriya na hasarar miliyoyin Naira sakamakon cin hanci da ya yi katutu a kasar

Nigeria Änderung der Wähung Naira
Hoto: Ubale Musa/DW

 Masharhanta dai sun yi hasashen cewar Najeriya kan yi hasarar bilyoyin Naira  a  lokaci kankani sanadiyar cin hanci da karban rashawa wanda da ya yi katutu  tsakanin 'yan kasar musamman manyan jami'an gwamnati, don haka suke kallon  cewar muddin  aka cigaba da wannan tafiya, to da alamu za'a kai  gabar da kasar za  ta kasa motsawa.