1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin jabun takardun satifiket na Atiku

Uwais Abubakar Idris AH
October 14, 2023

A Najeriya wata takadama ta sake kuno kai a kan takardar kammala karatun sakandire na dan takarar neman shugabancin Najeriya Atiku Abubakar.

https://p.dw.com/p/4XPWl
Nigeria I Atiku Abubakar I PDP
Hoto: Uwais Abubakar Idris

Wata sabuwa ce ta sake bullo a game da zarge-zarge da ma nunawa juna ‘yar yatsa tsakanin bangaren shugaban Naeriyar da na dan takarar neman shugabancin jam'iyyar adawa ta PDP a kan batun zargi na takardun karatu na jabu, inda bayan da ‘yan PDP ke doki na sun yi babban kamu, sai gashi suma 'yan APC sun bayyana bankado abin da suka kira jabun takardar kammala sakandire Malakar dan takararjam'iyyar PDP .

Tinubu da Atiku su dukkaninsu suna zargin juna da takardun karatu na jabu

Bola Tinubu da Atiku Abubakar
Bola Tinubu da Atiku Abubakar

Zargi ne dai na mai dokar barci ya buge da gyangyadi inda bangaren j jam'iyyar APC mai mulkisuka bayyana bankado zargi na samun sabani a takardar kammala sakandire na dan takarar neman shugaban kasar Atiku Abubakar, inda a takardar aka ga Sadeeq Abubakar yayin da dukkanin sauran ilahirin takardunsa ke dauke da sunan Atiku Abubakar. Tuni Atiku Abubakar ya musanta zargin. Wannan na faruwa ne a dai dai lokacin da kurar da ta taso a kan zargin gabatara da takardun shaidara karatu na boge da Atiku Abubakar da jami'yyarsa ta PDP ke ci gaba da tirkewa musamman dagewa na gabatar da wannan a matsayin shaida a kotun kolin Najeriyar da ke shari'ar kalubalantara zaben shugaban Najeriya. Ga mutane da dama na jefa tambaya a kan illar da wannan za yi ga Najeriyar a matsayin kasa da yadda ake kalon wadanda suke ko dai shugabanni ko kuma suke kokari na  kai wa ga madafun. Amfani da takardun jabbu dai babban laifi ne a dokar Najeriya. A yanzu za'a sa ido a ga yadda kotun kolin Najeriyar zab ta raba gardama a kan wannan batu, wanda lokaci ne kawai ake jira.