1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila: Al'umma na neman Benyamin Netanyahu ya yi marabus

Abdourahamane Hassane
January 21, 2024

A birnin Tel Aviv, dubban jama'a sun yi gangami domin neman firaminista Benjamin Netanyahu da ya yi marabus. sannan da neman a maido da mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.

https://p.dw.com/p/4bVSG
Hoto: Bonot Alternativa

 Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya jaddada adawarsa ga samun 'yancin Falasdinu a matsayin kasa mai cikakken yanci, yana mai cewa dole ne Isra'ila ta ci gaba da kula da harkokin tsaro a yankin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada. A tattanawar da suka yi ta waya tarho da shugaban  Amirka Joe Biden,Netanyahnu ya shaida masa cewa Dole ne Isra'ila ta tabbatar da cewa Gaza ba ta zaman wata barazana ba ga Isra'ila. A halin da ake ciki a  birnin Tel Aviv, dubban jama'a sun yi gangami domin neman a maido da mutanen da aka yi garkuwa da su tun ranar bakwai ga watan Oktoba a zirin Gaza, da kuma neman firaminista Benjamin Netanyahu da ya yi marabus, wanda ake zargi da ci gaba da yin yaƙin domin  neman ci gaba da yin mulki.