1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mali ta ce ba martaba dokar jinkirta ficewa daga ECOWAS ba

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 7, 2024

A ranar 28 ga watan Janairun da ya gabata ne Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar suka sanar da ficewarsu daga ECOWAS, sakamakon fama da takunkuman karya tattalin arziki daga kungiyar a dalilin juyin mulkin sojoji

https://p.dw.com/p/4c955
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Kasar Mali ta ce babu wani dalili da zai tilasta mata martaba dokar jinkirta ficewa daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS har tsawon shekara da dokokin kungiyar suka tanadar, kuma ta riga ta fice kenan.

Karin bayani:ECOWAS: Burkina Faso ta sanar da ficewa a hukumance

Wannan na cikin sanarwar gwamnatin mulkin sojin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito a yau Laraba.

karin bayani:Martanin kasashe kan ficewar wasu daga ECOWAS

A ranar 28 ga watan Janairun da ya gabata ne dai kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar suka sanar da ficewarsu daga ECOWAS, sakamakon fama da takunkuman karya tattalin arziki daga kungiyar a dalilin juyin mulkin sojoji.