1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Nijar: Takaddama kan amfani da kudin CFA

Gazali Abdou Tasawa ZMA
February 1, 2024

Mahawara ta kaure tsakanin ‘yan Nijar kan matsayin rarrabuwar kawuna tsakanin kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso kan ci gaba da amfani da kudin CFA bayan ficewa daga ECOWAS.

https://p.dw.com/p/4bwDs
Hoto: Francis Kokoroko/REUTERS; ORTN - Télé Sahel/AFP/Getty; Mikhail Metzel/TASS/picture alliance

Wannan ya biyo bayan kalamai masu akasi da juna da firaministan Mali da kuma shugaban kasar Burkina Faso suka furta kan wannan batu.

A wata fira da Firamnistan kasar Mali Abdoulaye Diop ya yi da manema labarai a lokacin wata ziyara da ya kai a kasar Togo, bayan ficewar kasashen kungiyar AES na Mali Burkina Faso da Nijar daga kungiyar CEDEAO, ya bayyana cewa kasarsa ta Mali za ta ci gaba da zama a kungiyar kasashen masu amfani da tsarin kudin bai daya na CFA wato UEMOA.

Banknoten CFA Francs
Hoto: SEYLLOU/AFP

Sai dai daga na shi bangare shugaban hukumar mulkin sojan Burkina Faso Ibrahim Traore, a wata fira ta musamman da ya yi da wata kafar yada labarai, ya bayyana cewa bayan ficewar kasashensu daga kungiyar ECOWAS yana kyautata zaton mataki na gaba da za su dauka shi ne na ficewa daga kungiyar ta UEMOA da kuma dakatar da amfani da kudin CFA.

Wadannan kamalai masu kama da cin karo da juna ta sanya wasu sun dora ayar tambaya kan yiwuwar soma samun sabani a tsakanin kasashen na AES kan batun kudi kasa da mako daya bayan ficewarsu daga kungiyar ta CEDEAO. Malam Siraji Issa na kungiyar MOJEN na daga cikin masu irin wannan tunani.

To sai dai Malam Aboubacar Kado masanin ilimin tattalin arziki a Nijar na ganin babu wani sabani da ke da akwai a tsakanin wadannan kasashen uku na Nijar Mali da burkina Faso kan aniyarsu ta ficewa daga kungiyar UEMOA da kuma samar da kudinsu na kansu.

Kamerun Währung
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Amma wasu ‘yan Nijar na ganin babu mamaki cikin sabanin da aka fara samu a tsakanin kasashen uku na AES kan maganar kudi, shirin da Malam Zabeirou wani dan jarida mai sharhi kan harkokin yau da kullum a Nijar ke ganin da wuya kasashen su iya aiwatar da shi.

Yanzu dai ‘yan Nijar sun kasa kunne suna sauraran matsayar da hukumomin mulkin sojan kasar ta Nijar za su dauka kan wannan batu na ci gaba da zama a kungiyar ta UEMOA ko kuma ficewa daga cikinta domin kafa sabon kudinsu na bai daya mai suna Sahel Da kasashen na Mali da burkina Faso.