1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon salon yaki da cin hanci a Najeriya

Uwais Abubakar Idris Abdoulaye Mamane(ZUD)
January 10, 2024

A daidai lokacin da ake bankado laifukan cin hanci da rashawa tsakanin jami'an gwamnatin Najeriya, hukumar yaki da cin hanci ta kasa ICPC ta lashi takobin kara zurfafa bincike a fanin

https://p.dw.com/p/4b4kP
Shugaban Najeriya Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola TinubuHoto: Gbemiga Olamikan/AP/dpa/picture alliance

Wani sabon salo ne na dakile matsalar cin hanci da rashawa a Najeriyar da ta zama tamkar ciwon ajali da baya jin magani, duba da abubuwan da suka faru a gwamnatin Shugaba Tinubu, inda cikin 'yan watanni aka zargi jami'anta da badakalar karakatar da biliyoyin kudi, a cikin yanayi da ya tada hankalin dukkanin alummar kasar, sanin irin gargadin da aka yi musu da ma abinda ya kamata, amma kuma duk ya kasa yin tasiri.

Karin Bayani:  Bincike a kan wata minista a Najeriya bisa zargin cin hanci

Sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, Dr Musa Adamu Aliyu, ya bayyana cewa "Mayar da hankali wajen rigakafin matsalar da hukunta masu laifi ne kawai mafita." Ana ci gaba da samun karin bayanai kan badakalar cin hanci da rashawa da ake zargin an tafka a ma'aikatara jinkai ta Najeriya, hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta gayyaci shugabanin bankuna guda uku na Najeriya, da suka hada da Jaiz da Zenith da Providend, saboda bayanan da ake ci gaba da bankadowa kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi.

Wasu jaridun Najeriya na wallafa labarai kan ayyukan hukumar EFCC
Wasu jaridun Najeriya na wallafa labarai kan ayyukan hukumar EFCCHoto: DW/A. Kriesch

'Yan Najeriya na ci gaba gaba da nuna bukatar ganin an bi kadin wannan lamari na bincike don kaucewa rufa-rufa. Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ya bayyana alwashin hadin gwiwa da sauran hukumomi, don yin taron dangi ga wannan matsalar, duk da yake an dade ana yiwa hukumar kalo na wacce ta kasa maida hankali sosai a wannan aiki.

Karin Bayani:  Yunkurin dakile cin hanci a Najeriya na gamuwa da cikas

A yanzu ana sa ido kan yadda za ta kaya a wannan bincike, wanda sannu a hankali ake kara bankado wadanda ke da hannu a cin hancin da rashawa da ya faru a ma'aikatar jinkan Najeriya, wanda ake zargin ministoci biyu, tsohuwar minista Sadiya Umar Faruq da kuma sabuwar da aka dakatar Betta Edu da aikatawa