1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaVietnam

Shagaban kasar Jamus ya karkare ziyara a Vietnam

January 25, 2024

Shugaban kasar Jamus ya bayyana damuwa a game da kare hakkin dan'Adam a Vietnan a yayin wata ziyarar aiki da ya kai kasar.

https://p.dw.com/p/4beIu
Jamus ta damu da matsalar kare hakkin bil-adama a Vietnam
Jamus ta damu da matsalar kare hakkin bil-adama a VietnamHoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Yayin da yake jawabi a jami'ar hadin guwiwa ta Jamus da Vietnam da ke birnin Ho Chi, Frank-Walter Steinmeier ya ce duk da yake kasashen biyu na da manufofi daya a fannoni da dama, to amma da akwai wasu batutuwa da ke hana ruwa gudu a game da hulda mai inganci a tsakaninsu musanman batun tauye 'yancin 'yan jarida da 'yancin fadar albarkin baki da kasar ta yi kaurin suna a kai.

Dama dai a alkaluman kungiyar 'yan jarida ta kasa da kasa Reporters sans frontières, Vietnam na a matsayi na 178 a cikin jerin kasashe 180 inda aka fi tauye 'yancin fadar albarkacin baki a duniya. 

Karin bayani:Shugaba Biden zai ziyarci Vietnam 

Kafin ya karkare ziyarar mista Steinmeier ya karfafa fatan huldar cinikayya mai karfi a tskanin kasashen biyu tare kuma da bude tsarin kasuwancinsu da sauran kasashe don gina tattalin mai karfi wanda zai bayar da damar murmurewa daga tarnakin annobar korona da kuma yakin Rasha da Ukraine.