1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Korar jakadun kasashe daga Nijar

Binta Aliyu Zurmi
August 26, 2023

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, sun sanar da korar jakadun kasashen Najeriya da Jamus da Amurka biyo bayan kin halartar taron ministan harkokin kasashen ketare.

https://p.dw.com/p/4Vc1u
Niger | General Abdourahmane Tiani
Hoto: Balima Boureima/Reuters

Wannan na zuwa ne bayan fidda sanarwar dakatara da jakadan Faransa wanda shi ma ya ki halarta taron.

Sai dai Faransa ta yi watsi da bukatar sojajin kan wa'adin sa'o'i 48 da suka bawa jakadanta Sylvain Itte na ya tattara inasa-inasa ya bar kasar daga jiya Juma'a.

Kazalika a dayan hannun kuwa, majalisar sojojin Nijar karkashin jagorancin janar Abdourahamane Tiani ta umurci dakarunta na su zauna a cikin shirin ko ta kwana biyo bayan karuwar hare-hare da suke fuskanta.

Tun bayan juyin mulkin da sojin suka yi a watan da ya gabata, karuwar hare-haren da aka samu ya hallaka sojoji da dama, matsalar tsaron da suka ce na daya daga cikin dalilan da suka kawar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum.