1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

BRICS: Yawan mabobi domin ci-gaba

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 24, 2023

Kasashe mambobin kungiyar Kasashen da Tattalin Arzikinsu ke Bunkasa wato BRICS, sun amince da kara yawan mambobinta. Kasashen na BRICS sun bayyana wannan aniya tasu ne, a karshen taronsu da suka gudanar a Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/4VYDL
Afirka ta Kudu | Johannesburg | Taro |  BRICS | Sababbin Mambobi
Shugaba Vladmir Putin na Rasha, a taron BRICS na bana ta hanyar bidiyoHoto: Sergei Bobylev/dpa/picture alliance

Shugabannin kungiyar Kasashen da Tattalin Arzikinsu ke Bunkasa wato BRICS da suka hadar da Brazil da Rasha da Indiya da Chaina da kuma Afirka ta Kudu, sun tattauna tare da amincewa da batun karbar sababbin mambobi a kungiyar a kokarin da take na samun karfin fada a ji a duniya. 

Tun da fari dai an samu sabani a tsakaninsu, inda Indiya ta nuna kin amincewarta. Sai dai daga bisani, Indiyan ta bayyana cikakken goyon bayanta na samun karin mambobin da rahotanni suka ce kasashe kimanin 40 sun mika bukatunsu na shiga kungiyar.

Kungiyar ta BRICS ta amince da kara mambobi shida, wadanda suka hadar da Ajantina da Masar da Iran da Habasha da Saudiyya da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa. Tarayyar Najeriya dai, na daga cikin kasashen da aka yi fatali da bukatarsu ta shiga wannan kungiya da ke shirin yin gogayya da sauran kungiyoyi masu fada a ji a fannin tattalin arziki a duniya.