1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya kaurace wa mahawarar 'yan takarar Republican

Binta Aliyu Zurmi
August 24, 2023

An fafata a mahawarar 'yan takarar neman shugabancin Amurka na babbar jam'iyyar adawa ta Republican ba tare da tsohon shugaban kasar Donald Trump ba.

https://p.dw.com/p/4VWYN
TV-Debatte der US-Republikaner
Hoto: Morry Gash/AP/picture alliance

Donald Trump da ke zama dan takara na gaba-gaba a jam'iyyar, sauran 'yan takarar 8 da ke neman tikitin jam'iyyar na bukatar sake lale a kan wanda zai jagoranci Republican a zaben shekarar 2024.

A cewarsu Trump na kara yin bakin jini a kasar kuma ba za su iya tunkarar babban zaben da zai ba su nasara a haka ba.

Gaba a wannan Alhamis Donald Trump zai mika kansa ga mahukunta a Georgia domin fuskantar shari'ar tuhumar da ake yi masa kan zargin yunkurin murde zaben shekarar 2020 a jihar.

Ko a ranar Laraba lawyansa da wasu mutum biyu sun mika kansu ga mahukuntan na Georgia bisa zargin rawar da suka taka a wancan zaben.

Wannan dai shi ne karo na hudu da ake tuhumar Trump tun watan Afrilu, hakan kuma ya sa shi zama tsohon shugaban kasa na farko a tarihin Amurka da ke fuskantar tuhume-tuhume a matakai da dama.