1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Abbas da Blinken sun magantu kan yakin Hamas da Isra'ila

Mahmud Yaya Azare Abdoulaye Mamane(ZUD)
January 10, 2024

Babban sakataren harkokin wajen Amurka na ci gaba da rangadi a kasashen yankin Gabas Ta Tsakiya, a kokarinsa na kawo karshen yakin Isra'ila da Hamas

https://p.dw.com/p/4b5Z3
Jagoran Falasdinawa Mahmud Abbas da Antony Blinken a birnin Ramallah
Jagoran Falasdinawa Mahmud Abbas da Antony Blinken a birnin RamallahHoto: Saul Loeb/AP Photo/picture alliance

A ci gaba da rangadin da yake a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya a kokarinsa na dakatar da yakin Hamas da Isra'ila, babban sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya isa a birnin Ramallah, don ganawa da shugaban Falalsdinawa Mahmud Abbas, yadda a yayin ganawar aka samu sa in sa tsakaninsu, bayan da sakataren Amurka ya yaba wa Isra'ila kan murkushe Hamas, tare da gayyatar gwamnatin Mahmud Abbas da ta maye gurbinta a zirin na Gaza.

Inda ya ce "Tunkarar makiyan da ke buya cikin fararen hula da masalatai da asibitoci suna harbi, abu ne mai matukar hatsari. A yanzu anyi nasarar kakkabesu. Ba mu lamunta da shirin Isra'ila na sake mamaye Zirin Gaza ba, don haka dole hukumar Falalsdinawa ta jagoranci gudanarwa a Gaza, don inganta rayuwar al'ummarsa wadanda a zamanin mulkin Hamas take yin garkuwa da su."

Karin Bayani:  Blinken ya gana da shugaban Falasdinawa

Falasdinawa na zanga-zanga a birnin Ramallah a yayin ziyarar Antony Blinken
Falasdinawa na zanga-zanga a birnin Ramallah a yayin ziyarar Antony BlinkenHoto: Issam Rimawi/Anadolu/picture alliance

Sai dai shugaban hukumar Falasdinawa Mahmud Abbas, ya sake jaddada irin jawaban da ya yi a Isra'ila da adawar Amurka inda ya bayyana cewa "Ku Amurkawa kuna cewa a fatar baki mu ne masu mulki da yankin Falalsdinu, bayan kun hada baki da Isra'ila kun kare da al'ummar Falalsdinawa, me ya rage mana da za mu mulka, bayan duk kun barmu a matsayin al'ummar da bata san me ke makomarta ba?"

Karin Bayani:  Ministar harkokin wajen Jamus tana Isra'ila

Dubban Falalsdinawa sun yi zanga-zangar adawa da ziyarar babban sakataren harkokin wajen na Amurka, wasu da dama sun daga kwalayen da a jikisa aka rubuta kalamun kakkausar suka ga Isra'ila da Amurka, a yayin da a hannu guda, shuwagabanin Masar da na Falalsdinun suka hadu da Sarkin Jodan a birnin Amman.