1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Ruto ya shakara guda a mulki

September 14, 2023

Yayin da shugaban kasar Kenya William Ruto ya cika shekara guda a kan karagar mulki, galibin 'yan kasar na kuka dangane da yadda tattalin arzikin kasar ya tabarbare a karkashin mulkin nasa.

https://p.dw.com/p/4WM86
Kenya | Shugaban Kasa | William Ruto | Shekara Guda
Shugaban kasar Kenya William Ruto Hoto: Khalil Senosi/AP/picture alliance

Duk da cewa da dama daga al'ummar kasar ta Kenya na kokawa kan tabarbarewar tattalin arziki da matsin rayuwa a yayin da Shugaba William Ruto ya cika shekara gudan, wasu magoya bayansa na cewa ana yi wa shugaban gajen hakuri. Kididdiga ta baya-bayan nan ta nuna cewa, a karon farko cikin shekara guda ta mulkin Shugaba Ruto an samu saukin hauhawar farashin kayayyaki a kasar Kenya. A watan Agustan da ya gabata Shugaba Ruto ya bugi kirjin cewa gwamnatinsa ta fito da wasu tsare-tsare da za su hana kasar ta karbo rance daga ketare a nan gaba, domin yana yi wa kasar kyakkyawan tanadi saboda gaba.

Kenya | William Ruto  | Shekara Guda | Tsadar Rayuwa | Zanga-Zanga
Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a kasar KenyaHoto: John Ochieng/SOPA/ZUMA/IMAGO

Sai dai duk da wannan kwarin gwuiwa da Shugaba Ruto ke nunawa, radadin tsadar rayuwa na ci gaba da gigita al'ummar kasar ta Kenya saboda tashin gwauron zabin da kayan masarufi suka yi. Mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Nairobi Evans Sandagi ya ce, shugaban nasu na bukatar lokaci domin cimma nasara. Wani binciken jin ra'ayin jama'a da aka fitar a wannan makon, na nuna yadda galibin 'yan Kenya suka gamsu cewa a cikin shekara guda Shugaba William Ruto ya rude ya kasa gano bakin zaren matsalolin da suka yi wa tattalin arzikin kasar daurin huhun goro. Sai dai kuma ba, komai ba ne ya lalace a kasar ta Kenya a cikin shekara guda ta mulkin William Ruto. A cewar Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF, kasashe biyar da tattalin arzikinsu ke bunkasa a cikin hanzari sun hada da Angola da Habasha da Najeriya da Afirka ta Kudu da kuma Kenyan.