1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotunan Najeriya na ci gaba hukunci kan zaben jihohi

November 24, 2023

A ranar Juma'ar ne kotu a Abuja ta tabbatar da wanda ya lashe zaben gwamna a Kaduna da ke Najeriya. Siyasar jihohi dai na daukar hankali watanni shida bayan kafuwar gwamnatoci.

https://p.dw.com/p/4ZQHg
Babbar kotu a Najeriya
Babbar kotu a NajeriyaHoto: Reuters/T. Adelaja

Kotun daukaka kara da ke a Abuja babban birnin Najeriya ta tabbatar wa Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC a jahar Kaduna kujerarsa.

Duk da cewa an barbaza jami‘an tsaro a cikin kwaryar Kaduna don zama cikin shirin ko-ta-kwana gabanin kotun ta yanke hukuncin.

Kotun daukara kara mai zama a Abuja babban birnin kasar ce ta tabbatar da nasarar Gwamna Uba Sani na jam‘iyyar karkashen jam'iyyar APC na jahar Kaduna a matsayin wanda ya lashe zaben da ake gudanar a jahar bayan sauraran dukkan korafe-korafe da hujjojin da aka gabatar mata.

A Kaduna dai harkokin kasuwanci da zirga-zirgar alumma na ci gaba da wakana cikin kwanciyar hankali da lumana, lamarin da ke nuna cewa jama'a da dama na gudanar da harkokinsu.

Tuni dai 'yan jam'iyyar PDP masu adawa suka yi watsi da hukuncin kotun na Abuja.