1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Mahmud Yaya Azare LMJ
November 27, 2023

A daidai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wutar kwanaki hudu tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas a yankin Zirin Gaza ke karewa, masu ruwa da tsaki sun yi kokarin ganin bangarorin biyu sun amince da tsawaita wa'adinta.

https://p.dw.com/p/4ZVJF
Isra'la | Gaza | Tsagaita Wuta
Falasdinawa da motocin marasa lafiya, na ficewa daga Gaza bayan tsagaita wutaHoto: Ibraheem Abu Mustafa/REUTERS

Bayan musayar fursinoni da kuma sakin wadanda kungiyar Hamas ke garkuwa da su, yarjejeniyar tsagaita wutar ta kuma bayar da damar shigar da kayan agaji yankin na Zirin Gaza. Kasashen duniya dai sun yi ta yin matsin lamba ga bangarorin biyu kan tsawaita wa'adin tsagaita wutar, domin a samu a 'yantar da illahirin wadanda Hamas ke garkuwa da su a kuma shigar da wadatattun kayan agaji cikin yankin na Zirin Gaza. Tun da fari dai, shugaban Isra'ila Isaac Herzog ya ce gwamnatinsa ta lamunta da duk wani tsagaita wutar da zai kai ga sakin karin wadanda kungiyar Hamas din ke garkuwa da su.

Karin Bayani: Tsagaita wuta na kwanaki hudu a Gaza

Hamas din da ke rajin fafutukar yaki da mamayar Isra'ila a Falasdinu da wasu kasashen Yamma suka ayyana a matsayin ta ta'adda, ta ce tana yin gagarumin yunkuri na ganin an saki karin Falasdinawa ko da bayan an kawo karshen yarjejeniyar ne kana mai bai wa hukumar Falasdinawa shawara kan lamuran diflomasiyya ya nunar da cewa, burinsu bai takaita ga tsagaita wuta mai kayyadadden wa'adi ba. Shima shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da ke ziyarar nuna goyan baya ga Isra'la, ya ce tsagaita wutar domin dalilan agaji kusan wajibi ne kan Isra'ilan. A cewarsa Hamas ce ta jawo sake tsunduma yankin cikin yaki, kuma ita kadai ya zama wajibi a zarga kan bala'in da ya shafi Isra'ila da al'ummar Falasdinawa.

Isra'la | Isaac Herzog | Ziyara | Shugaban Kasa | Jamus | Frank-Walter Steinmeier
Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da shugaban Isra'la Isaac HerzogHoto: Ronen Zvulun/AP Photo/picture alliance

Matsin lambar kasashen duniya yana karuwa ba kawai a kan a tsawaita wa'adin yarjejeniyar dakatar da fada a Gaza ba, har ma da samun sabon yunkuri wajen lalubo hanyar warware rikicin da ake fama da shi tsakanin Isra'ila da Falasdinawan. A nasa bangaren mataimakin shugabar Hukumar Tarayyar Turai EU Josep Borrell ya ce, kafa wata kasar Falasdinawa a Gabar Yamma da Kogin Jordan da Kudus da kuma Gaza zai tabbatar da zaman lafiya da tsaron Isra'ila. Bugu da kari firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na ci gaba da shan suka, kan dagewar da yake na ci gaba da yaki ko da bayan an gama 'yanto illahirin wadanda Hamas ke garkuwa da su.

Karin Bayani: Matsayar Jamus a rikicin Isra'ila da Hamas

Firaministan kasar Spaniya Pedro Sánchez na daga cikin masu sukar, inda ya ce kisan kan mai uwa da wabi da Isra,ila kewa fararen hular Falasdinawa da galibinsu kananan yara ne da mata abu ne da ba za a lamunta ya ci gaba ba domin hakan ne ke jawo mayar da martanin da ke hana zaman lafiya a yankin. Tarzoma ba ta haifar da komai, sai dai karin tashin hankali. Shi ma firaministan Belgium Alexander De Croo ya nunar da cewa, ci gaba da ragargaza Gaza abu ne da ba zai taba sabuwa ba domin abun kunya ne da takaici ace duniya za ta zura ido taga ana yi wa wata al'umma haka.