1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayar Jamus a rikicin Gabas ta Tsakiya

November 16, 2023

Rawar da Jamus take takawa a rikicin yankin Gabas ta Tsakiya tsakanin Isra'iala da kungiyar Hamas, na da alaka da dangantaka ta musamman da Jamus din ke da ita da Isra'ila.

https://p.dw.com/p/4YtEW
Jamus | Olaf Scholz | Ziyara | Isra'ila | Benjamin Netanyahu
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da firaministan Isra'ila Benjamin NetanyahuHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Sai dai wannan dangantaka ta musamman da Jamus din ke da ita da Isra'ila, ba ta hana ministar harkokin wajen Jamus din Annalena Baerbock neman mafita tare da kusan duk wanda ke iya ba da tasa gudunmawa wajen wareware rikicin ba. Tafiya na yin tafiya kuma al'amura na kara daburcewa, wannan shi ne irin tunanin da Baerbock ke da shi a kan rikicin na yankin Gabas ta Tsakiya. Tun farkon rikicin kawo yanzu dai, ministar harkokin wajen Jamus din sau uku tana kai zyarar aiki a yankin.

Karin Bayani: Isra'ila za ta shiga sabon babi na yaki a Zirin Gaza

A ziyararta ta baya-bayan nan, Baerbock ta ziyarci Isra'ila da yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Saudiyya. Burin Jamus dai shi ne taimaka wa fararen hula da ke shan wahala a yankin Zirin Gaza da kuma kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su daga hannun Hamas, bugu da kari tana son taimakawa wajen kaucewa rikicin ya zama na yanki baki daya. Gwamnatin Tarayyar Jamus ta yi tsayin daka kan tsaron Isra'ila, amma a hannu guda ta yitir da karuwar hare-hare da Isra'ila ke kai wa a Gaza.

Zirin Gaza | Hari | Isra'ila | Masunta
Yadda jiragen yakin Isra'ila suka yi barin wuta a kan jiragen ruwan masunta a Zirin GazaHoto: Ashraf Amra/AA/picture alliance

Firaministan Falasdinu Mohammed Schtajjeh ya koka da kakkausar murya game da Jamu saboda ta tallafa wa Isra'ila da makamai, abin da ya ce yake kara mata kwarin gwiwar ci gaba da kai hare-hare kan al'ummar Gaza. A farkon wannan shekarar Jamus da Isra'ila sun amince da aikewa da wasu jiragen ruwa na karkashin teku guda uku na Jamus. Hatta batun tsagaita wuta a zirin Gaza, na da muhimmanci ga diflomasiyyar Jamus. Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz shi ma ya sha yin watsi da kiran tsagaita wuta, a ganinsa yana da muhimmanci "Isra'ila ta yi nasara a kan Hamas."

Karin Bayani: Gaza zai iya ruruta rikicin Isra'ila da Hezbollah

Ganawa da wakilan kasashen Larabawa irin su Saudiyya da Qatar na da muhimmanci, a lokacin tafiye-tafiyen na Baerbock. Dukansu biyun masu shiga tsakani ne masu tasiri, misali idan ana maganar kubutar da mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su. Wannan gaskiya ne musamman ga Qatar, saboda Doha ba gida ce kadai ga shugabannnn Hamas ba, tana daya daga cikin manyan ma su ba ta kudi. A halin da ake ciki Jamus ta kara yawan tallafin jin-kai ga yankunan Falasdinawa a bana daga  Euro miliyan 38 zuwa miliyan 160, saboda halin a aka samu kai a ciki sakamakon rikicin.